Wani hamshakin Attajiri yayi ma marasa galihu tagomashi
Shugaban kamfanin mai na Stanel, Mista Stanley Uzochukwu ya raba ma mata da mazajensu suka rasu da marayu da dama kayayyakin abinci da na amfanin yau da kullum a garin Abuja da jihar Filato.

Yayin da take nuna godiyar tag a halin arziki irin na Mista Uzochukwu, Hannatu Danladi, shugaban kungiyar zawaran cocin ECWA dake Tudun Wadan jihar Filato tace “nayi mamaki matuka dangane da kirkin Stanley Uzochukwu musamman yadda yake taimaka ma gajiyayyu da marayu. Shine mutum daya tilo daya tallafa mana muke samun saukin radadin tattalin arzikin da ake fuskanta, wannan shine karo na 3 ko na 4 dayake kawo mana ziyara tun 2011.”
KU KARANTA:Yadda wani matashi ya tsira daga wani mummumar hatsarin mota
Hannatu ta cigaba da fadin: “Ba ziyara kawai yake kawo mana ba, zuwa yake yi da manyan Tireloli cike da kayyakin abinci daban daban, kamar su man gyada, shinkafa, masara, sabulai, zannuwa, suga da makamantansu. Muna fatan sauran masu kudi zasu yi koyi da shi, kuma muna mai addu’ar Allah ya kara masa arziki.”

Shima wani maraya daya amfana da tagomashin Mista Stanley Uzochukwu, Idoko James ya mika godiyarsu a madadin sauran daruruwan marayun da suka amfana.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng