Rashin Imani: Uba ya banka ma ýaýansa mace da namiji wuta (Hotuna)

Rashin Imani: Uba ya banka ma ýaýansa mace da namiji wuta (Hotuna)

An gurfanar da wani magidanci mai suna Endris Mohammed dan shekaru 46 gaban kuliya manra sabo kan tuhumarsa da aikata laifin kisan yayan sa guda biyu Saros Endris da Leanor Endris ta hanyar banka ma gidansu wuta yayin da suke cikin gidar.

Rashin Imani: Uba ya banka ma ýaýansa mace da namiji wuta (Hotuna)
Saros da Learnor

An kama Endris ne yayin da yayi kokarin hallaka matarsa kuma uwar yayansa Penil Teklehaimanot, an kama shi ne a cikin wata konanniyar mota a garin Newcastle na kasar Ingila a ranar 28 ga watan Oktobar bara.

KU KARANTA:Gwamna Ganduje ya kaddamar da ginin katafaren shagun zamani a jihar Kano

Rashin Imani: Uba ya banka ma ýaýansa mace da namiji wuta (Hotuna)
Endris Mohammed

An gurfanar da Endris gaban kotu ne jim kadan bayan fitowarsa daga asibiti inda yayi jinyar kunar daya samu a jikinsa, dan sanda Sajan Nick Bernes ya bayyana cewar yaran mutumin na cikin barci a dakinsu ne tare da mahaifinnasu lokacin da mahaifin nasu ya sulala ya fita kuma ya banka ma gidan wuta.

Rashin Imani: Uba ya banka ma ýaýansa mace da namiji wuta (Hotuna)

Da kyar makwabtansu suka iya fitar da yayan nasa Saros mai shekaru 8 da Leanor mai shekaru 6, inda suka garzaya dasu asibiti, inda a can ne aka tabbatar da mutuwarsu.

Yansandan West Midland sunce za’a gurfanar da mahaifin yaran a gaban kotun majistri dake Walsall.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng