Yan kato-da-gora sun kama yan Boko Haram 3 a jihar Zamfara

Yan kato-da-gora sun kama yan Boko Haram 3 a jihar Zamfara

Sarkin Zurmi na jihar Zamfara ya mika ma wasu yayan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram ga jami’an rundunar Sojar kasa, bayan an kama su a masarautarsa.

Yan kato-da-gora sun kama yan Boko Haram 3 a jihar Zamfara

Babban kwamandan runduna ta 223 dake jibge a garin Gusau, Kanal Abdullahi Adamu ya tabbatar da kama yayan kungiyar ta Boko Haram, inda yace a yanzu haka suna garkame a hannunsu, kuma har ma sun aika dasu babban rundanar sojoji ta daya dake Kaduna don cigaba da gudanar da bincike.

KU KARANTA:Yanzu Yanzu: Boko Haram ta kashe mutane 8, ta sace mata 7 a yayin kaddamar da wani hari a jihar Barno

Kamfanin dillancin labarai NAN, ta ruwaito cewar matasa yan kato-da-gora ne suka samu nasarar kama yan Boko Haram din.

Kanal Abdullahi Adamu ya lissafa wasu daga cikin makaman da aka kama a hannun yayan kungiyar ta Boko Haram sun hada da bindigu kirar AK-47, alburusai, layu, da sauran kayan maye.

“Bayan gudanar da binciken farko, muna gano wadandan aka kama suna da alaka da yayan Boko Haram din da suka tsere daga dajin Sambisa tun bayan kwato shi daga hannun su.” inji shi.

Daga karshe Kanal Abdullahi yayi ma Sarkin Zurmi tare da matasan kato d agora godiya dangane da kokarin da suke yin a ganin sun kawat da miyagun mutane a tsakaninsu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel