Yadda aka gina wani kogo inda aka binne Al-Qur’ani miliyan 2.5 a Pakistan (Hotuna)
An samu wani bawan Allah dan kasuwa daya tattaro Qur’anai guda miliyan biyu da rabi (2.5million) wadanda aka daina amfani dasu a kasar Pakistan inda ya gina musu dakin adana tun a 1992.
Shi dai wannan dan kasuwa mai suna Samad Lehri ya yanke shawarar gina wannan ma’adana ne daya sanya ma suna ‘Jabaal-e-Noor-‘ wato ‘dutsen haske’ bayan ya lura da yadda ake wulakanta tsoffin Qur’anai da dama a kasar ta Pakistan.
KU KARANTA:Ta rubuta Al-Qur’ani gaba daya da tawadan ruwan Zinari
Wannan kogo da ake ajiye Qur’anai yana da tsawon kilomita 3.5, kuma rahotanni sun bayyana cewar akwai Qur’ani mai shekaru 600 ajiye a ciki, kuma har yanzu ana sake gina wasu hanyoyin duk a cikin kogon dutsen don fadada shi sakamakon ana samun karuwar yawan Al-Qur’anai dayawa.
Doka ne dai a addinin musulunci a wulakanta Qur’ani, hakan ya sanya dakin ajiyar ma’adana daya dace da tara Qur’anan. Sanadiyyar wannan ya sanya jama’a da dama sukan zuwa wannan kogo don yawon bude ido, kuma su gane ma kansu ba jiyau ba.
Ga bidiyon Qur’anan:
mai karatu idan kana da shawara ga masu gudanar da wannan aiki, zaka iya samun su a news@tuko.co.ke
Asali: Legit.ng