Gaskiya daya ce inji wani fasto

Gaskiya daya ce inji wani fasto

Shugaba Elijah ya bukaci shugabannin addinai su zama masu gaskiya a kowani lokaci.

Gaskiyane
Fasto Elijah

Babatunde Elijah wanda shi ne Baban firist ta Inri Evangelical Church ya kira shugabanin addinai da babban murya cewa duk wani shugaba mai sha'awar yin siyasa ya fito ya yi siyasar maimakon boyewa a karkashin sunan addini.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Elijah kuma ya yi kira ga shugabanin addinai cewa su kasance a shirye domin gabatar da mafita ga matsalolin kasar.

Ya ce, ya kamata shugabannin addinai su kazance masu fada wa al’umma gaskiya ko da yaushe a yin da kasar ke fuskanci matsaloli daban daban.

KU KARANTA KUMA: ‘Yan Shi’a da dama sun samu rauni

Shugaban ya yi magana ne game da rikicin kudancin Kaduna, kuma ya ce wajibi ne gwamnati ta samar da tsaro.

Babu wata addini da ke goyon bayan tashin hankali. A matsayin mu kirista, rayuwa na da matukar muhimmanci kuma babu wani mai izini dauka rayuwa dan uwarsa.

Shugaban ya shawarci gwamnati ta hukunta duk wani maluki da ke goyon bayar tashin hakali a kudancin Kaduna , idan ba haka ba babu shaka za a iya maimaita a nan gaba.

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa

http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng