An rataye wani dan sarki bisa umurni uban sa

An rataye wani dan sarki bisa umurni uban sa

- Kasar Kuwait ta zartar da hukuncin kisa a kan wadansu fursunoni bakwai, ciki har da dan gidan sarautar kasar; wannan ne dai hukunci irinsa na farko tun bayan shekarar 2013

- An dai rataye su ne a babban kurkukun kasar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Kuna ya bayyana daga wata sanarwa

An rataye wani dan sarki bisa umurni uban sa
An rataye wani dan sarki bisa umurni uban sa

Kotu ta samu Yarima Faisal Abudallah Al Jaber Al Sabah ne da laifin kisan kai da kuma mallakar makami ba bisa ka'ida ba.

Haka kuma a cikin fursunonin da aka kashe akwai 'yan kasar Philippines da Masar da Habasha da kuma Bangladesh.

An dai same su ne da aikata manyan laifuka da suka hada da kisan kai da yunkurin kisa da satar mutane da kuma fyade.

Shi dai yariman kotu ta same shi da laifin kisan wani yariman kasar ne a shekarar 2010.

Editan BBC a yankin Gabas ta Tsakiya, Sebastian Usher, ya ce ko da yake ba bakon abu ba ne, amma ba kasafai ake daure 'yan gidan sarauta ko kuma zartar da hukuncin kisa a kansu ba.

Ya kara da cewa wannan hukuncin na nuni da cewa babu wani wanda ya fi karfin doka.

Cikin wadanda aka ratayen har da wata mata Nusra al-Enezi wadda 'yar kasar ce, kuma an same ta ne da laifin cinna wuta a tantin da ake walimar auren amaryar da mijinta ya yi.

Wutar ta kai ga mutuwar mutane fiye da 50.

Bugu da kari, a cikin wadanda aka aiwatar da hukuncin a kansu har da wadansu 'yan aiki 'yan asalin Philippine da kuma Habasha wadanda aka samu da laifin kashe wasu daga cikin 'yan gidan da suke wa aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng