Yan Najeriya sun yi jimamin mutuwar wata jarumar Soja mace
Tun bayan bayyanar labarin mutuwar wata gwarzon jarumar soja a yan kwanakin nan ne jama’a da dama daga sassan kasar nan suke jajinta ma iyalan sojan tare da tausaya musu.
Ita dai Blessing Ene Edache kurtun soja ce a rundunar mayakan sojan kasa na Najeriya, kuma ta gamu da ajalinta ne sakamakon zazzabin cizon sauro, hakan ya sanya wani da yayi ikirarin shine mahaifinta ya nuna damuwarsa a fili, cike da alhini.
KU KARANTA:Dogo na Daura ya gamu da dogon Soja (Hotuna)
Shima mahaifin nata, wanda soja ne mai igiya biyu, wato Laftanr Prince C Okafor ya ce “yata ta kaina ta rasu.”
Soja Blessing ta rasu tana da shekaru 23, kuma za’a binne ta ranar Juma’a 27 ga watan Janairu a garin Adoka dake jihar Binuwe.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng