Abun da China keyi da naman jaki zai baka mamaki (Karanta)
- 'Yan sanda a kasar Afirka ta kudu sun gano wasu 'yan China masu fatauci da kasuwancin fata da naman jaki.
- An gano fatar jaki sama da 5,000 a cikin wani wurin ajiya a wata gona da ke kusa da birnin Benoni a lardin Gauteng.
Babu wanda aka kama amma masu binciken suna fatan cewa ma'aikatan gonar za su iya gane wadanda ke aike wa da fatun a cewar jaridun Mail da Guardian.
An tara kuma aka boye fatun, wanda aka wanke tsaf da gishiri a bayan wasu tsoffin kujeru da wasu kayan aikin gona.
KU KARANTA KUMA: Tsohon ministan kwadago ya koma jam’iyyar APC
China tana amfani da sinadarin gelatin da ake samu a jikin jaki wajen hada magunguna da magungunan kara ni'imar mata da kuma mayukan hana alamun tsufa.
Kasuwancin wanda ake yi a halasce kuma wasu lokutan a haramce na da darajar miliyoyin daloli, sai dai yana barazana ga yawan jakai da ke wasu kasashen Afirka.
A bara ne dai Najeriya da Burkina Faso suka hana fitar da jakai daga kasashen.
Ba wannan ne karon farko da bukatar da China ke yiwa jakuna ke jawo ce-ce-ku-ce a baya-baya nan ba.
A watan Satumbar da ya gabata ne dai Nijar ta hana fitar da jakai, inda ta yi gargadi cewa ninki da aka samu a kasuwancin yana barazana a yawan jakunan da take da su.
Sinadarin gelatin da ake samu daga jikin jaki na matukar tsada a China a matsayin wani sinadarin magani wanda ke inganta jini da kara karfin garkuwar jiki da kuma kara kuzari.
A wasu lokutan ana kiransa "Three nourishing treasure".
KU KARANTA KUMA: Zaben Gwamnan Jihar Anambra: Soludo yaci damara
Ana samar da sinadarin gelatin da ya yi fice ne a wani yankin da ke Arewa maso Kudancin lardin Shandong, inda ake yin sa da ruwan rijiyar garin.
Ana hada Sinadarin gelatin da wasu 'yan'yan itatuwa da abinci mai kara jini a sayar da shi a matsayin abin kwadayi.
Asali: Legit.ng