An haifi wani jariri a kasar Indiya mai kafa 4 mazakuta 2 (Hotuna)

An haifi wani jariri a kasar Indiya mai kafa 4 mazakuta 2 (Hotuna)

Wani abin al’ajabi ya faru a kasar India, inda wata mata ta haihi jariri da kafafu hudu, mazakuta guda biyu.

An haifi wani jariri a kasar Indiya mai kafa 4 mazakuta 2 (Hotuna)

Mahaifiyar jaririn ta yi farin ciki matuka, inda tace wannan baiwa ne daga Allah, don haka zata tabbatar da sama mai isashshen kulawa, kuma ba zata yi wani kokarin canza mai halitta ba. “yaron da muka haifa na farko kimanin shekaru uku da suka gabata lafiyansa kalau, sai dai mu talakawa ne, don haka ba zamu iya daukan dawainiyar jaririn ba a asibiti.” Inji mahaifiyar.

KU KARANTA:Dogo na Daura ya gamu da dogon Soja (Hotuna)

Likitan daya gudanar da aikin tiyata wajen cire jaririn yace ya tattauna da abokanan aikinsa kwararru a bangaren tiyata, sunce lallai yaron na bukatar karin tiyata don ya zamto kamar kowane mutum.

An haifi wani jariri a kasar Indiya mai kafa 4 mazakuta 2 (Hotuna)

Sai dai daga bisani mahaifiyar jaririn tace “likitoci sun bani shawarar a wuce da yaron babban asibitin VMS don cigaba da samun kulawa tare da duba lafiyarsa, don haka a yanzu ina fatan ya samu lafiya, ya zama kamar kowan mutum.”

Wani likita dake can asibitin VMS yace “a yanzu haka kwararrun likitocin tiyata suna lura da halin da yaron ke ciki, amma da alama babban lamari ne.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng