Wani jariri sabon haihuwa yazo da wani abin mamaki a goshinsa (HOTUNA)

Wani jariri sabon haihuwa yazo da wani abin mamaki a goshinsa (HOTUNA)

Wani mutum Murat Engin da matarsa Ceyda Engin sun samu haihuwar jariri mai suna Cinar wanda yazo da wani shaidan tambarin zuciya a goshinsa.

Wani jariri sabon haihuwa yazo da wani abin mamaki a goshinsa

Hakan ya sanya aka lakaba ma jaririn sun ‘dan soyayya’ sakamakon zanen zuciya shine tambarin soyayya, amma a gaskiya yaron yana da matukar kyawun halitta.

KU KARANTA:Ana amfani da jarirai wurin kunar-bakin-wake

Wani jariri sabon haihuwa yazo da wani abin mamaki a goshinsa

Mahaifin jaririn, shi ne ya fara lura da zanen dake goshin jaririn nasu yayin dayake wanke shi bayan haihuwarsa.

“Bayan unguwarzoma ta kammala wanke jaririn, sai na hangi wannan tambari bisa goshinsa, dana matso kusa sai naga tambarin yayi daidai da zanen zuciya, hakan ya sanya hawaye zuba daga idanu na.” Inji mahaifin.

Wani jariri sabon haihuwa yazo da wani abin mamaki a goshinsa

A yanzu watannin jariri Cinan 14, kuma ya shahara a kasar Turkiyya, inda mutane ke tururuwar zuwa don daukan hoto tare da shi. Mahaifin Cinan yace koda yaushe zuka je asibiti sai likitoci da sauran ma’aikatan asibitin su yi ta kiran sunansa suna daukan sa.

Wani jariri sabon haihuwa yazo da wani abin mamaki a goshinsa

Mahaifin ya kara da cewa babu wanda aka taba haifa da tambari a danginsu, don haka yana ganin alamar sa’a ce tare da yaron.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng