Abubuwan da suka faru a Najeriya karshen mako
Kamar yau da kullum , Jaridar Legit.ng bata gushe tana tattaro muku muhimman labaran abubuwan da suka faru a Najeriya a karshen makon da ya gabata.A sha karatu lafiya
1. Mahaifi ya nanawa yaronsa karfen wuta a duwawu saboda yana luwadi
A jihar Borno ne wani diraktan wata ma’aikata a jihar Borno wanda aka sakaye sunansa,ya shiga hannun jami’an yan sanda da laifin nanawa haifaffen cikinsa karfe dafa ruwan zafi a duwawunsa saboda yaron na luwadi.
2. Anyi garkuwa da shugaban karamar hukuma a Maiduguri
Jaridar Premium Times ta bada rahoton cewa wasu yan bindiga sunyi garkuwa da Modu Guja,shugaban karamar hukumar Bama a jihar Borno.
3. Dalilin da yasa na dau na annabawa - Yahya Jammeh
Tsohon shugaban kasar Gambiya, Yahya Jammeh,yayi maganarsa na farko tun lokacin da aka tabbatar da cewa ya amince zai sauka daga karagar mulki.
4. Anyi ram da dan sanda mai satan yara,ya sayar N600,000
An damke wani kofuran yan sanda mai suna Uche Odoemena,wanda akafi sani da Prince a jihar Imo. Majiya ta bayyana wa jaridar Punch cewa a ranan Alhamis,19 ga watan Junairu, an damke da sandan ne a Okigwe kuma an kaishi Owerri a ranan Laraba, 18 ga Junairu.
5. Soji, ’yan sanda, DSS, NSCDC sun mamaye garin Kano
Wasu manyan jami’an tsaro rike da muggan makamai wanda ya kunshi Soji, ‘Yan sanda, DSS, NSCDC sun watsu a wurare masu dari a jiya. Yan sanda sun bayyana wannan ata’sa’I a matsayin yunkurin na duba yiwuwan kai hari garin. Wasu manyan hanyoyi da ya bi gidan gwamnain jihar, filin jirgin sama da ofisoshin tsaro,duk an kulle su.
6. Farashin man diesel na kara hauhawa
A Najeriya tsadar man diesel ko kuma man gas na cikin abubuwan da ke addabar masu sufuri musamman na manyan motoci da masu kanana da matsakaitan masana'antu har ma da wasu kamfanoni da ke sarrafa kayayyaki.
7. TO FA! An kai harin kunar bakin wake a Saudiyya
Wasu ‘yan harin kunar bakin wake guda biyu sun hallaka a birnin Jeddah na Saudiya, bayan tarwatsewar bama baman da suke rataye da su, yayin musayar wutar da suka yi da jami’an tsaron kasar.
https://twitter.com/naijcomhausa
https://web.facebook.com/profile.php?id=510888295754238
Asali: Legit.ng