Dan Juma-da-dan Jummai? Yan shi'a sun ziyarci Bishop a Sokoto

Dan Juma-da-dan Jummai? Yan shi'a sun ziyarci Bishop a Sokoto

Yan kungiyar yan uwa Musulmi mabiya koyarwar Shi'a Ta IMN dake jihar Sakkwato sun ziyarci babban Bishop din darikar Katolika na birnin Shaihu Rabaran Mathew Hassan Kuka, da nufin samar da fahimtar juna tsakanin bangarorin biyu. Yayin da a daya bangaren' yan Shi'ar ke fuskantar tsangwama daga wani sashi na Musulmi, saboda bambancin akida.

Dan Juma-da-dan Jummai? Yan shi'a sun ziyarci Bishop a Sokoto
Dan Juma-da-dan Jummai? Yan shi'a sun ziyarci Bishop a Sokoto

A wani labarin kuma, Babban limamin reshen kungiyar Nasrul-Lahi-l Fatih (NASFAT) dake babban birnin tarayya Abuja Alhaji Sharafudeen Abdulsalam Aliagan ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta sakin jagoran kungiyar 'yan uwa Musulmi ta Nijeriya Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, domin samar da dorewar zaman lafiya da kiyaye adalci.

Limamin kungiyar ya yi wannan kira ne a yayin wata ziyara da ya kai babban ofishin buga jaridun Daily Trust, tare da wata babbar tawaga ta mabiyansa, inda ya yabawa kamfanin bisa kokarin da suke yi na buga fassarar hudubar Jumma'a a cikin jaridar Aminiya da kamfanin ke bugawa mako mako.

Ya ba da shawarar cewa, ya kamata gwamnati ta gudanar da kyakkyawan bincike game da harkokin kungiyar, domin a samu fahimtar juna tsakanin bangarorin biyu.

"Ya kamata gwamnati ta bi hanyar ruwan sanyi don warware wannan matsalar, ta sake El-Zakzaky. Ba ma son a samu wata damuwa a kasar nan, saboda cigaba da tsare da ake yi, musamman ma tun da kotu ta yanke hukunci game da batun," a cewar Aliagan.

Limamin ya kuma bayyana takaicin sa na ganin duk da irin kokarin da mai alfarma sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci, Alhaji Sa'ad Abubakar lll, yake yi don ganin an samu hadin kai a tsakanin Musulmi, har yanzu sai cigaba da samun rabuwar kai ake yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng