Sarkin Kano yace baiwa mace Ilimi yafi gina masallatai

Sarkin Kano yace baiwa mace Ilimi yafi gina masallatai

San Kano, Alhaji Muhammadu Sunusi II ya bayyana damuwarsa kan yadda hamshakan attajira da dama ke yawan turo masa da takardan neman izini don gina masallaci a maimakon su taimaka wajen ilimantar da yara mata.

Sarkin Kano yace baiwa mace Ilimi yafi gina masallatai
Sarkin Kano yace baiwa mace Ilimi yafi gina masallatai

Sarki Sunusi ya bayyana haka ne a yayin taron tsarin hadahadar kudi a muslunce da cibiyar binciken akan bankin musulunci na jami’ar Bayero ta Kano ta shirya (IIIBF), inda yace wannan ne dalilin daya sanya yankin Arewa maso yamma zamantowa koma baya a fagen cigaba da tattalin arziki.

KU KARANTA: Mun gamsu da kokarin sojin Najeriya wajen gano yan matan Chibok -Masu fafutuka

“Na gaji da yadda mutane ke zuwa suna fada min wai zasu gina masallaci, kun san haka muke a Arewa, sai muyi ta gina masallaci, alhali mun bar yayan mu mata a cikin jalici. Don haka ina rokon attajirai, idan kuna so ku taimaka ka jihar Kano, kada ku zo min don neman izinin gina masallacin naira miliyan 300, saboda muna da masallatai da yawa a Kano, amm idan kana so ka taimake mu, ka je ka ilimantar da yarinya mace a kauye.

“wannan shine dalilin daya sanya muke kan gaba a jahilci, aure da wuri, mutuwar aure da rikice rikice daban daban kuma aka bar mu a baya wajen cigaba.” Inji San Kano.

San Kano yace idan dai muna son magance wannan matsalar, toh lallai sai mun fara kokarin ilimantar da yaran talakawa. “Ya kamata jama’a su gane dole sai mun canja halin mu, idan ka duba alkalumman kiwon lafiyar mata, matan da suke daukan ciki kafin su kai shekaru 15 sun fi mutuwa a wajen haihuwa fiye da matan da suka dauki ciki a shekara 20. Don haka ya zama wajibi akan mu mu sake duba maganan auren wuri.

“Idan ka dubi alkalumman da kyau, zaka ga cewra kashi 45 na matayen dake tsakanin shekaru 15-19 a yankin Arewa maso yamma duk sunyi aure, amma abin takaici shine kashi 75 na matayen dake wannan rukunin basu iya karatu ba da rubutu, jahilai ne. ya Ilahi, ku fada min wace irin al’umma ce wannan?”

Daga karshe San Kano ya kiraye gwamnati data gina karin makarantu tare da samar da malamai musamamn don fuskantar ilimin mata, ta yadda makaratu masu zaman kansu zasu taimaka ma gwamnati a inda ta gaza.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel