An damke mutum yana hakan kaburbura a makabarta( Hotuna)

An damke mutum yana hakan kaburbura a makabarta( Hotuna)

An damke wani boka mai suna Isiaka Isah, mai hakan kabari yana daukan gawawwaki a makabartan Karaworo Angwan tiv a jihar Kogi.

An damke mutum yana hakan kaburbura a makabarta( Hotuna)
An damke mutum yana hakan kaburbura a makabarta( Hotuna)

Yan banga sun damke Isah yayinda yake hakan kabarin ne a cikin makabartan a ranar Talata, 10 ga watan Janairu.

A cewar wani marubucin Facebook, Mofiinternational Usman, wanda ya halarci inda abin ya faru kuma ya watsa labarin a shafinsa, yace an mika shi ga hukumar yan sanda kafin mutan unguwa su hallaka shi.

Usman wanda yace yayi masa tambayoyi yace mutumin yace wani boka ne ya fada masa ya birne wani abu cikin makabartan saboda fatalwa ya daina binsa.

KU KARANTA: Abubuwa 7 da baka sani game da Barrow ba

Karanta abinda ya rubuta:

"Sunanshi Isiaka Isah, an damke shi ne yana hakan kaburbura a makabartan Karaworo Angwan tiv a jihar Kogi da safiyar nan. Baccin an farga da wuri , da matasan unguwa sun aikashi lahira, amma lokacinda nayi masa tambayoyi, yace niyyarshi shine ya birne abu ba wai hakan gawawwaki ba. Kana ya kara da cewa yana wasu muggan mafarki ne cewa fatalwa na binsa wanda ya say a je wajen wani boka wanda yace masa yaje ya birne wadannan abubuwa. Da aka ce masa ya ciro abinda ya birne, yace bai san inda ya birne suba.”

Saboda kiyaye irin wannan abu, kwamitin makabartan na neman taimako domin a zagaye magabartan, ana iya taimakawa ta asusun bankin da ke kasa:

"Account Name: Karaworo cementary project."

"Account Number: 2087223237."

"Bank Name: U.B.A."

Allah saka da alheri

Domin karin bayani ku biyomu a shafinmu na Facebook da Twitter https://www.facebook.com/naijcomhausa/

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng