Kisa kan kuskure: Shugaban sojojin saman Najeriya yayi magana
A daidai lokacinda Najeriya ta tabbatar da rasuwar mutane 70 da kuma 100 da suka ji rauni sanadiyar kuskuren da mayakan saman kasar suka yi da suka jefa ma sansanin 'yan gudun hijira bam da zaton 'yan Boko Haram ne, hafsan mayakan saman AVM Sadiq Abubakar ya bayyanawa manema labaru cewa abun da ya faru kaddara ne.
Yayinda yake yiwa manema labarai bayani babban hafsan sojojin mayakan sama na Najeriya AVM Sadiq Abubakar yace babu wani sojan sama da zai fita da jirgin yaki da zummar cutar da mutane.
Yace rahoto suka samu cewa mutanen dake wurin 'yan Boko Haram ne suke taruwa saboda haka sojojin saman suka fita su kare rayukan mutane amma kuma lamarin ya kasance ba haka ba ne, ya shiga wani halin da basu yi zato ba. Yace suna juyayin hakan da ya faru.
Harin da sojojinsa suka kai a Rann cikin jihar Borno sun kai ne bisa kuskure sanadiyar rahoton da suka samu.
Inji AVM Abubakar kuskuren ba zai sauya salon yakin da su keyi ba saboda ba nufinsu ba ne su kashe mutane haka kawai ko su ci mutuncinsu ko su musguna masu ba. Manufarsu ita ce tabbatar da cewa sun kare rayukan al'umma da dukiyoyinsu. Yace zasu saurari abun da bincike zai nuna masu.
AVM Abubakar yace mayakan biyu da suka je da jirgin duk sun samu cikakken horo domin ko bayan da suka koyi tukin jirgi a Najeriya an turasu Amurka inda suka kara samun horo suka kware a aikin kuma sun sha yin abubuwan da suka kare rayukan mutane. Sun kakkashe 'yan ta'ada a wurare daban daban.
Asali: Legit.ng