Mahaukaciya ta haihu a bakin titi a jihar Ogun (Hoto)

Mahaukaciya ta haihu a bakin titi a jihar Ogun (Hoto)

Wata mata Ubi Eze da aka tabbatar mahaukaciya ce tuburan ta haihu a ranar Alhamis 12 ga watan Janairu, inda ta haifi ɗa namiji a kan titin Arepo na jihar Ogun.

Mahaukaciya ta haihu a jihar Ogun (Hoto)
Mahaukaciya ta haihu a jihar Ogun (Hoto)

Wani mazaunin unguwar Mista Akinlolu Akinsanmi daya garzaya da mahaukaciyar zuwa asibiti ya bayyana cewar da misalin karfe 6 na safiyar Alhamis ne ya tsinci matar kwance male-male cikin jini a gefen hanya tare da jaririn nata sabon haihuwa.

KU KARANTA:Labarin wani mutum mai nauyin kilo 435, yana kalaci da ƙwai 36, nama kilo 3 da madara lita 5

Akinsanmi yace koda ya karaso inda matar take akwai mutane biyu dake tsaye a kanta, da zuwansa sai yace musu suje su nemo motar daukan marasa lafiya, amma shiru shiru basu dawo ba, hakan ya sanya shi rugawa wani asibiti mafi kusa, inda ma’aikatan asibitin suka biyo shi da keken guragu wanda aka yi amfani da shi wajen garzayawa da matar asibitin.

Jama’an yankin Arepo sun bayyana cewar sun hangi matar yana yawan shigowa a yan kwanakin da suka gabata. Amma ita ma mai jegon tayi magana, inda tace takowa tayi a kasa daga yankin Majidun na garin Legas har zuwa jihar Ogun.

Sa’annan ta kara da cewa wani saurayinta ne ya fatattake ta daga gidansa bayan yaki amincewa da shine yayi mata ciki, sai dai matar ta kara da cewa ita bata ma san yadda aka yi ta samu cikin ba.

Toh fa jama’a menen abin yi?

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng