Labaran da suka girgiza Najeriya a ranan Laraba
Kamar yau da kullum , Jaridar Legit.ng bata gushe tana tattaro muku muhimman labaran da suka girgiza Najeriya a ranan Labaran,17 ga watan Junairu, 2017. A sha karatu lafiya
1. Rundunar sojin Najeriya sun fasa kasar Gambiya
Kungiyar ECOWAS ta baiwa shugaban kasar Gambiya Yahaya Jammeh wa’adin ranan Alhamis 19 ga watan Junairu ya sauka ko kuma a cire shi da karfin soja.
2. EFCC ta kwace jirgin tsohon gwamnan jihar Borno, da wasu yan siyasa 2
Jihar Borno ta kasance hedkwatan yan ta’addan Najeriya a shekarun da ya gabata wanda kuma wannan jiha ta fuskanci hare-hare, hallakan daruruwan rayuka;mata da yara, wanda ake sa ran rashin kulan gwamnati ne akan abu da kuma rashawa ya sabbaba haka.
3. Shekaru 4 kenan babu wuta a garin Godluck Jonathan – Mutanen Otuoke
Otouke wata kauye ce a karamar hukumar Ogbia a jihar Bayelsa kuma garin tsohon shugaban kasan Nejariya, Goodluck Jonathan.
4. Gwamnatin jihar Kaduna ta sa dokar ta baci a awa 24 a Zangon-Kataf
Gwamnatin jihar Kaduna ta sake sanya dokar ta baci na awa 24 a karmar hukumar Zngon Kataf a kudancin jihar sanadiyar wata sabuwar rgima da ta barke.
5. Da yiwuwan za'a rantsar da Adama Barrow a wajen birnin kasar Banjul
Ministan harkokin wajen Najeriya,Mr Geoffrey Onyeama, yace da yiwuwan za'a rantsar da shugaban kasar Gambiya mai jiran gado Adama Barrow a wajen Banjul, babban birnin kasar.
6. Ka sauka daga mulki yanzu ko.... - Amurka ga Jammeh
Kasar Amurka ta fadi ma Jammeh cewa ya sauka daga mulki ga wanda ya lashe zaben da aka gudanar ranan 1 ga watan Disamba.
Asali: Legit.ng