Jirgin sama ɗauke da ɗimbin gwala-gwalai yayi hadari a kasar Zimbabwe

Jirgin sama ɗauke da ɗimbin gwala-gwalai yayi hadari a kasar Zimbabwe

Wani jirgin sama mallakan wani attajiri dauke da tarin gwalagwalai yayi hatsar a kasar Zimbabwe yayin dayake kan hanyar fita daga sararin samaniyar kasar.

Jirgin sama ɗauke da ɗimbin gwala-gwalai yayi hadari a kasar Zimbabwe

Jirgin na kamfanin Central Air Traffic Services yana dauke da gwala gwalan da suka kai nauyin kilo 22, wanda darajan su ta kai dala 800,000, kimanin (N392,000,000) ya fado ne a garin Kennilwonwort.

KU KARANTA: Ta haifi yan hudu bayan kwashe shekaru 7 bata haihu ba

Sai dai ba’a san takamaimen inda jirgin ya nufa ba, kuma ba’a san daga ina suka samo gwala gwalan ba. Amma kamfanin jirgin tace jirgin na dauke da gwalagwalan wani kamfani ne mai zaman kansa.

Jirgin sama ɗauke da ɗimbin gwala-gwalai yayi hadari a kasar Zimbabwe

Hukumar kula da sufurin jiragen kasar Zimbabwe ta bayyana cewar akwai matukan jirgi su biyu a cikin jirgin kirar Cessna 206, kuma basu samu wasu manyan raunuka ba, sakamakon hukumar sojin saman Zimbabwe ta aika da jirage masu tashin angulu guda biyu don gudanar da aikin ceto a wajen da hadarin ya faru.

Ita dai kasar Zimbabwe tana da arzikin gwal sosai a kasa, sai dai jama’a da dama na ganin mahukuntar kasar ne kadai da attajiran kasar, sai kuma turawa ke morar arzikin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel