Labarin wani mutum mai nauyin kilo 435, yana kalaci da ƙwai 36, nama kilo 3 da madara lita 5
An samu wani mutumin kasar Pakistani sarkin karfi wanda keda tsawo kamar bishiyar giginya, nauyinsa kuma ya kai kilo 435, kwatankwacin nauyin buhunan siminti 9 kenan.
Shi dai wannan sarkin karfi sunan sa Arbab Khizer Hayat, shekarunsa 25 kuma yana yin karin kumallo da kwai guda 36, madara lita biyar da nama kilo 3, da safe kenan kawai.
KU KARANTA:Dalibin jami’ar Maiduguri ya ƙera ƙaramar mota mai aiki da ƙwaƙwalwa
Sai dai Arbab wanda tun yana dan kankani ya fara yin kiba, yace baya jin alamar rashin lafiya ko kadan a dalilin kibarsa data wuce misali, kai Arbab cewa yayi babban burinsa shine ya zamto mutumin daya fi kowa karfi a Duniya.
“babban burina in lashe kyautan kambun wanda yafi kowa karfi a duniya, ina yi ma Ubangiji Allah godiya daya bani wannan kibar, ina sa ran nan bada dadewa ba zan shiga wasannin daga karfe, don haka dole in cigaba da yin kiba ina yin karfi.” Inji Arbab.
Arbab yace yana daukan nauyin daya kai kilo 4500 a gasar daga karfe daya gudana a kasar Japan, sa’annnan yana fatan nan bada dadewa ba zai shiga gasar kokawa da ake yi a kasar Amurka wato WWE.
Mutane da dama suna zuwa gidan Arbab don gane ma idonsu halittarsa tare da daukan hotuna da shi, saboda idan Arbab yana jin wasa, toh daura mai motar tarakta ake yi ko wasu kananan motoci don ya ja su, har sai ya gaji!
Asali: Legit.ng