Sakonni 5 da Shekau ya aika ma shugaba Buhari

Sakonni 5 da Shekau ya aika ma shugaba Buhari

Shugaban kungiyar yan ta’adda na Boko Haram Abubakar abu Muhammad Shekau ya sake fitowa cikin wani sabon faifan rikodin.

Sakonni 5 da Shekau ya aika ma shugaba Buhari
Sakonni 5 da Shekau ya aika ma shugaba Buhari

An jiyo muryar Shekau ne a sabon rikodin din yana bugun kirji, inda ya dauki alhakin kai harin da aka kai na kunar bakin wake a masallacin jami’ar Maiduguri, wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar wani Farfesa guda da sauran masallata a jiya Litinin 16 ga watan Janairu da asuba.

KU KARANTA:Rundunar sojan sama tayi luguden wuta a mafakar yan Boko Haram

Sai dai Shekau bai kammala batutuwan sa ba sai da ya aika ma shugaba Buhari wasu sakonnin kart a kwana, kamar haka:

1-‘Ka mutu da bakin ciki’: Shekau ya fara bude bayaninsa ne da albishiri ga shugaba Buhari da sauran kafatanin musulman kasar nan da cewa sai sun mutu da bakin cikin Boko Haram, toh fa! Inda aka jiyo shi yana karanto wasu ayoyin Al’Qur’ani.

2-‘Ka tuba’: Abubakar Shekau ya kara kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari daya tuba zuwa ga Allah, idan yayi haka toh zasu shirya, zasu zama yan’uwa na kud da kud.

3-‘Bana jin haushinka’: Jagoran yan ta’addan Boko Haram ya shaida ma shugaban kasa Muhammadu Buhari cewar shifa baya jin haushinsa, kawai dai yana yin abin da yake ganin ya kamata ne.

4-‘Kai ba sa’an fada na bane’: Haka zalika Shekau ya sake jaddada ma shugaba Buhari cewa bai isa yayi fada da shi ba, don shi da karfin Allah yake fada bada karfin soji ba, Shekau yace Buhari yayi duk abinda zai yi, amma ba zai kama shi ba.

5-‘Bani ke fadan ba’: Shekau ya karkare sakonnin daya aika ma shugaban kasa Buhari da cewa shi fa bada karfin shi yake yaki ba, a’a. yace karfin Allah Ubangijin talikai ne. don haka a kada a raya ba zai mutu ba har sai Allah yayi, kuma a cewarsa ai ayoyin Allah sune suka koya masa jihadi.

Ku saurari muryar Shekau a nan:

Asali: Legit.ng

Online view pixel