Wannan dan wasan ya fi kowa daraja a nahiyar Turai (Karanta)
- Wani bincike ya gano cewa dan kwallon Barcelona Neymar na matakin na daya cikin jerin 'yan wasan tamaula da suka fi daraja a Turai, wanda ya kai fam miliyan 216
- Wata cibiyar nazarin kwallon kafa ce ta gudanar da binciken inda ta yi la'akari da kudin da aka sayi dan kwallon da tsawon yarjejeniya da ya kulla da kuma shekarun dan wasa
Nazarin ya ce Neymar ya fi abokin wasansa na Barcelona, Lionel Messi daraja, wanda kuɗinsa ya kai fam miliyan 149.
Paul Pogba wanda Manchester United ta saya a matsayin wanda ya fi tsada a fagen tamaula kan kudi fam miliyan 89, yana darajar fam miliyan 136.4.
Cristiano Ronaldo, wanda ya lashe Ballon d'Or da kyautar gwarzon dan kwallon kafa na duniya na Fifa yana mataki na bakwai da mai darajar fam miliyan 111.
Gareth Bale yana matsayi na 14 da darajar fam miliyan 73.8, kasa da kudin da Real Madrid ta saye shi fam miliyan 85.3 a shekarar 2013.
Wasu 'yan wasan Ingila da ke cikin jerin goman farko sun hadar da Harry Kane na Tottenham mai darajar fam miliyan £122 da kuma Dele Alli mai fam miliyan 96.
Asali: Legit.ng