Ya kashe abokinsa saboda kwaɗayin naman kare

Ya kashe abokinsa saboda kwaɗayin naman kare

Wani matashi mai suna Sunday Hycenth mai shekaru 27 ya hallaka abokinsa Onwe Ozoemelem kan rikici data faru a tsakanin su game da farfesun naman kare.

Ya kashe abokinsa saboda kwaɗayin naman kare
Ya kashe abokinsa saboda kwaɗayin naman kare

Jaridar Punch ta ruwaito lamarin ya faru ne a garin FESTAC, inda Hycenth da abokinsa suka dambace kan farfesun naman kare da wani abokinsu ya siyan musu.

KU KARANTA:Ýan Boko Haram sun fille kawunan mutane 16 a Kamaru

Rahotanin sun bayyana cewar shi dai Hycenth ya yi ma abokinsa kulli ne a kirji, inda nan da nan abokin Onwe ya yanke jiki ya fadi, sai dai koda aka garzaya da shi asibiti ya cika.

Ashe Hycenth yayi shuka a idon makwarwa, nan da nan yansandan FESTAC suka yi caraf da Hycenth, inda suka mika shi ga sashin kula da miyagun laifuka na hukumar yansandan jihar Legas dake Yaba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel