Wasikar wani soja zuwa ga abokin aikinsa da aka kashe a yakin Boko Haram

Wasikar wani soja zuwa ga abokin aikinsa da aka kashe a yakin Boko Haram

- Sakamakon yakin da dakarun sojojin Najeriya suke da yan Boko Haram a yankin Arewa maso gabas, hakan yayi sanadiyyar rasuwar sojojin da dama

- Wannan ya sanya wani soja aika ma abokinsa da aka kashe wasikar ban kwana, yana jaddada masa ba zasu fasa aikinsu ba

Ya Abokina,

Mu sojoji ne, kuma muna yaki don tabbatar da zaman lafiya, muna yin atisaye don kasancewa cikin koshin lafiya da kuzari, muna rayuwa ne don kashe miyagun mutane, dole ne mu kwato ma kan mu girma, babu wanda zai bamu a kyauta.

Wasikar wani soja zuwa ga abokin akinsa da aka kashe a yakin Boko Haram

Ka sani cewar bamu tsoron mutuwa, sai dai mu tare ta gaba da gaba. Abokina, ka sani cewar ba zamu taba mantawa da kai ba, tarihi ma ba zai manta da kai ba. Muma mua nesa da gida, bamu da abokin wasa sai makaman mu.Don haka mai zamu yi muji dadi idan ba kare kasar mu ta gado ba?

KU KARANTA:Bamu kama wani mutum farar fata a dajin Sambisa ba – Buratai

Duk da yake cewar ana mana kallon marasa galihu, amma duk da haka muna baiwa jama’a albishir, ba zamu taba gazawa ba wajen karya dukkan wanda ya zalunci al’umma. Zamu kwana a daji, mu hau ruwa mu bi iska duk don samar ma mutanen mu zaman lafiya.

Wasikar wani soja zuwa ga abokin akinsa da aka kashe a yakin Boko Haram

Zamu cigaba da yaki a bakin rayukan mu, zamu nutse a cikin rayuwa, kuma zamu fado daga jirgi duk don mu tabbatar da komai yayi daidai a tsakanin yan kasar mu, mu uku ne, amma abu daya ne. gaba dayan mu zamu gina kasa ingantacciya.

Ka huta lafiya dan uwana, ba za’a taba mantawa da kai ba. Allah ya albarkanci dakarun sojan kasa, dakarun sojan ruwa da dakarun sojan kasa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel