TASHIN HANKALI: Cutar murar tsuntsaye na bazuwa a Najeriya

TASHIN HANKALI: Cutar murar tsuntsaye na bazuwa a Najeriya

A Najeriya wata cutar murar tsuntsaye ta bulla inda a halin yanzu sama da kaji miliyan uku suka kamu. Ministan Ayyukan Noma da raya karkara na Najeriya, Chief Audu Obeh ya ce murar tsuntsayen ta bazu zuwa jihohi 26.

TASHIN HANKALI: Cutar murar tsuntsaye na bazuwa a Najeriya
TASHIN HANKALI: Cutar murar tsuntsaye na bazuwa a Najeriya

A wani labarin kuma, majalisar dattijai a Najeriya ta yi kira ga gwamnatin Tarayya ta janye dokar haramta shigo da motoci ta kan iyakokin kasar da ta soma aiki tun a 1 ga watan Janairu. Dubban mutane za su rasa ayyukan yi sakamakon daukar matakin, a cewar Majalisar.

Wasu Senatocin arewa ne suka gabatar da kudirin inda suka yi watsi da matakin haramta shigo da motocin ta kan iyakokin Najeriya na kasa.

Senatocin sun hada Shehu Sani daga Jihar Kaduna da Kabiru Gaya daga Jihar Kano wadanda suka danganta daukar matakin a matsayin rashin adalci ga Talakawa da ke cin abinci ta hanyar sana’ar Mota.

Sanata Kabiru Marafa daga Jihar Zamfara ya shaidawa majiyar mu ta RFI Hausa cewa gwamnati na iya saka haraji ga ‘Yan fito amma ba daukar matakin haramta shigo da motocin ba.

Ku biyo mu a Fezbuk: https://web.facebook.com/naijcomhausa/?_rdr

Ku biyo mu a tuwita: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng