Boko Haram: Mayaka 163 sun mika wuya cikin satin nan

Boko Haram: Mayaka 163 sun mika wuya cikin satin nan

- Rundunar sojojin Najeriya dake birnin Maiduguri dake fafatawa da 'ya'yan kungiyar Boko Haram tace ta samu nasarar cafke wasu mayakan Boko Haram su 163 kana wasu guda biyu suka mika kansu da kansu

- Kwamandan rundunar mai kula da yankin arewa maso gabashin Najeriya Manjo Janar Lucky Irabor ya shaidawa manema labarai na mako mako

Boko Haram: Mayaka 163 sun mika wuya cikin satin nan
Boko Haram: Mayaka 163 sun mika wuya cikin satin nan

Manjo Janar Irabor yace suna cigaba da samun nasarori da dama da suka hada da gano makamai daga hannun 'yan kungiyar tare da kame wasu daga cikinsu.

Sojojin sun kara yin arangama a kauyen Gulde da 'yan ta'adan a karamar hukumar Askira Uba inda suka kashe 'yan ta'adan su goma sha daya kana suka kama wasu tara da ransu, yayinda soja guda ya samu rauni.

Kawo yanzu sojojin sun samu gawarwakin 'yanuwansu goma sha biyar da suka bace can baya.

A yankin tafkin Chadi sojoji sun kashe 'yan ta'ada shida tare da cafke makamai masu dimbin yawa.

A wani taho mu gama da suka yi da 'yan ta'adan sojojin sun yi hasarar jami'ansu guda biyar kana sojoji uku suka samu raunuka.

Ku biyo mu a Fezbuk: https://web.facebook.com/naijcomhausa/?_rdr

Ku biyo mu a tuwita: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel