ABIN TAUSAYI: Mutane 5 suka hallaka a wata hatsarin wuta (HOTUNA)
Wani matashi mai suna Sarafa Lasisi da iyalinsa a garin Koko ta jihar Kebbi sun hallaka a wata mummunar hatsarin wuta a gidansu.
A ranar Talata, 10 ga watan Janairu 2017 ne wannan hatsarin ya auku a inda wani daga cikin ɗan'uwan matashin ya sanar da aukuwar hadarin a shafinsa ta Facebook. An rahoto cewa shi mutumin da matarsa da 'ya'ya uku ne suka hallaka a wannan hadarin.
Wani daga cikin dan’uwan marigayi kuma mai suna Don Baba ya wasa wasu hotunonin margayin a shafinsha a inda yake bankuana da marigayin.
Kuma wani mutum, Abdulrauff Mustapha, shi ma ya saka wasu hotunonin hadarin wutar a shafinsha.
Inda ya ke cewa: “Allah ya sa al janat Firdausi ne makomar sa da iyalansa Amin ya Allahu. Wannan babban asara ne ga duk dangin gaba daya.''
Lalle, wannan wata babbar asara ce!
Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa
http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng