Fafaroma ya bayyana su waye ainihin yan ta'adda (Karanta)
- Shugaban Darikar Katolika ta Duniya, Fafaroma Francis ya danganta masu kai hare-hare a fadin duniya a matsayin mahaukata da ke da tabin hankali tare da yin kira ga shugabannin addini da su fadada fatawar cewa, babu wanda zai yi kisa da sunan Ubangiji
- Fafaroma ya yi jawabin ne a lokacin da ya ke ganawa da jakadun kasashen duniya a fadar Vatican
A cikin jawabin nasa, Fafaroma Francis ya yi kira ga shugabannin kasashen duniya su yi kokarin yakar talauci da ke jefa mutane cikin wata rayuwa ta tsattsauran ra’ayin addini.
A cewar Fafaroma tsattsauran ra’ayi ne ya haifar da ta’addanci a kasashe Afghanistan da Bangladesh da Belgium da Burkina Faso da Masar da Faransa da Jamus da Iraqi da Jordan da Najeriya da Pakistan da Tunisia daa Turkiya har ma da Amurka.
Fafaroma Francis ya bada misali kan yadda ake kisan yara kanana a Najeriya da sunan adddini da kuma kai wa mutane hare-hare suna ibada da ma’aikata da matafiya a Masar da Brussels da Nice da Berlin da Santanbul.
Shugaban darikar ta katolika ya yi kira da babbar murya ga shugabannin addini su fadada fatawar kyamar kisan mutane da sunan addini tare da wa’azi ga mabiya na tsoron Ubangiji da nuna soyayya ga makwabci.
Fafaroma ya tabo batutuwa da dama da suka shafi zaman lafiya a rikicin Nukiliyar Korea ta Arewa da rikicin Isra’ila da Falasdinawa da rikicin Libya da Sudan ta Kudu da kuma tabbatar da mafaka ga dubban ‘Yan gudun hijira.
Asali: Legit.ng