Daliba yar ajin karshe a jami’ar Ife ta bace
- An alanta bacewar Miss Orjiugo Christiana Obumeke yayinda ba’a ganta bat un ranan laraba 4 ga watan Junairu
- Miss Orjiugo Christiana Obumeke ta kasance yar aji 5 a jami’ar Obafemi Awolowo university (OAU)
An alanta bacewar Miss Orjiugo Christiana Obumeke, wata yar aji 5 a jami’ar Obafemi Awolowo university (OAU) Ile-Ife, jihar Osun.
Jaridar LIB ta bada rahoton cewa Christiana ta tafiya ne zuwa Aba, jihar Abia domin cin bikin kirismeti, sai ta bar gida domin komawa makaranta ranan 4 ga Junairu, 2017.
KU KARANTA: Muhimman labaran ranan litinin
Game da cewar iyalanta, babu wanda ya samu labarinta har yanzu.
Ana rokon jama’ a cewa duk wanda ya samu labarinta ya tuntubi wadannan lambobi 08023016464, 08080888719, 08022480981.
A bangare guda, wani dalibin karatun likita na jami’ar Oluwaseun Olorunfemi, ya kwanta dama. Wannan ya faru ne ranan 20 ga watan Disamba yayinda wani direban mota yayi sama sama da shi. An kaishi asibiti inda yayi kwanaki shida kafin ya rasu a ranan 25 ga watan Disamba.
https://www.facebook.com/naijcomhausa
https://www.twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng