ABIN AL’AJABI: Sunan Allah ya fito a jikin itatuwan moringa
- An gano wasu itatuwa da rubutun sunayen Allah a jiki a gidan wasu kiristoci a wani gari mai suna Ado-Odo, Ota, jihar Ogun.
Wasu itatuwa moringa biyu a cikin wata titi sun zama abin kallo ga mutane a inda aka samu wasu rubuce-rubuce Arabic a jikin itatuwan.
Ana kwatata zato cewa wayanna rubuce-rubucen Arabic suna daya daga sunayen Allah ne. Masu wayanna gidaje sun bakanci duban mutane daga wurare daban-daban a dalili da wannan mujisa.
Wayannan itatuwa moringa masu rubutun sunayen Allah a gidajen wasu kiristoci guda biyu sun sama wata cibiyar shakatawa ga dubban mutane wayanda sun zo rokon Allah ne a wannan wurin.
Rahoton daga NAN na nuna cewa itatuwan moringa na wayannan gidaje ne ma su adireshi No.6, da kuma No.9, Unity Street, ire-akari Estate, Iloye, Abule Iroko, Ado-Odo Ota a Jihar Ogun.
Malam Michael Ibironke wanda yana daga cikin mazauni a daya daga cikin gidajen, yace ya yi fiye da shekaru 17 a wannan gidan kuma ya tabbatar da cewa an dasa itatuwan ne a shekara 2014.
Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa
http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng