Uwa ta gudu ta bar jariranta yan-biyu a Asibiti
A yan kwanakin da suka gabata ne wata mata mai suna Sarah Ademola tayi wani abin ban mamaki bayan ta gudu daga asibiti inda ta bar jariran ta yan-biyu data haifa, kuma har yanzu ba’a san inda ta shiga ba.
Mahaifin jariran Adeyemi Ademola yace ba zai yarda ya maida Uwargidarsa ba, koda ma ta dawo sakamakon watsi da yayansu da tayi a aisbiti, mijin yace gaba daya ma zai canza gida ne don kada ta gano inda suka koma.
KU KARANTA:Ya biya ma mazauna gidan yarin Kano su 25 kudin beli
Yayin da mijin matar ke yi ma yansanda jawabi a ofishin yansanda na Pedro dake unguwar Somolu, yace tun dama Sarah tayi mai karyar cewar yayanta biyu kafin suyi aure, amma yace sai bayan sunyi aure ne ya gano cewar yaya shidda take dasu ba biyu ba.
“Tun a ranar 16 ga watan Disambar bara ne mata ta tsere daga asibiti bayan ta haifi yan-biyu, sai yanzu kuma da na samu halin biyan kudin asibiti da ya kai N150,000 shine take nuna sha’awar dawowa. Tambayar da nake so in yi mata shine ‘me zata dawo ta yi? Bayan tace bata bukatan jariran.
“don haka nake ganin dawowarta zai zama barazana ga rayuwar jariran, don haka ba zan mayar da ita gidana ba. Abinda nake bukata shine jama’a su taimaka min don in rike yarana. Mata ta ta yaudareni tun kafin muyi aure inda tace min yayan ta biyu, sai bayan munyi aure ne na gane ashe yaranta shidda
“kuma ta fada ma kawayenta cewar ita bata bukatar jariran data haifa yanzu, saboda a cewarta ba zata iya dawainiyar yara takwas ba, don haka ne ma ta gudu ta bar jariran. Ina neman taimako don in samu wani gida daban don daki daya da nake ciki a yanzu ba zai dauke ni da jariran ba.
“rahotannin da ake yadawa wai uwargidar gwamnan jihar Legas ta bamu tallafi karyace, Sanata Gbenga Ashafa ne kawai sai wata kungiyar sa kai suka bamu tallafi.”
Ita ma shugabar asibitin Gloria Akinbobola tace sun so su sallami jariran, amma sakamakon tserewar mahaifiyarsu dole ys sanya suka fasa, amma tunda mahaifinsu yazo yanzu, zasu sallame su.
Ku bibiyi labaran mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko http://www.twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng