Don Allah, don soyayyar ma'aiki Sallallahu Alaihi Wa Sallam mu taimaka kan wannan yarinya
Akwai wata yarinya mai suna Fatima Jibril da kuma itace mai shekara 10 da ke fama da matsananciyar rashin lafiya a asibitin Murtala Muhammed na jihar Kano
Sau biyu ana yi mata tiyata sakamakon mummunan ciwon Taifot da ya lahanta jikinta.
Yanzu ana matakin yi mata tiyata kashi na uku, sai dai jikinta yayi galabaitar da aikin ba zai iyu ba. Don haka ana bukatar Naira Dubu Dari (100) domin saya mata magani kafin tiyatar. Sannan ko yaya taci abu yana fitowa ne ta inda aka yi mata aikin.
KU KARANTA: Gwamna Obiano zai kammala tituna 111 a wata uku
Shine ake neman kudin abincin mai magani a ciki. Mai N100, N200 zuwa sama da haka don Allah don soyayyar da muke wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam mu taimaka mu aika zuwa
Allah Ya biya bukata ga duk wanda ya taimaka ko daidai da yada wannan sako ne.
Mun dauki wannan labari daga shafin Facebook din na jaridar Rariya. Mu a gidan labaran Legit.ng ke yi sanarwar don Allah.
Ku karanta hakan kuma na karin bayani: https://www.facebook.com/naijcomhausa/photos/pcb.744320532411012/744320275744371/?type=3&theater
Ku kalli hotuna:
Asali: Legit.ng