Takaitaccen labaran abubuwan da suka faru jiya Alhamis
Har ila yau, jaridar Legit.ng bata gushe tana tattaro muku muhimmai da Takaitaccen labaran abubuwan da suka faru jiya Alhamis 5 ga watan Junairu, 2017 ba.
1. Kashe-kashen kudancin Kaduna: MASSOB ta sa baki
![Takaitaccen labaran abubuwan da suka faru jiya Alhamis Takaitaccen labaran abubuwan da suka faru jiya Alhamis](https://cdn.legit.ng/images/1120/vllkyt2ob16jhvpqa.jpeg?v=1)
Yayinda kashe-kashe ke cigaba da gudana a kudancin jihar Kaduna, Kungiyoyin yakin neman Biafra wato Movement for the Actualisation of the Sovereign States of Biafra (MASSOB) da Biafra Independent Movement (BIM),sunce kisan kiristoci a jihar Kaduna sinadarin raba kasan ne
2. Rahoton da ke yaduwa kan ranan daukan dalibai bogi ne - Hukumar NYSC
![Takaitaccen labaran abubuwan da suka faru jiya Alhamis Takaitaccen labaran abubuwan da suka faru jiya Alhamis](https://cdn.legit.ng/images/1120/vllkyt3rserlahlvo.jpeg?v=1)
Shugaban hukumar bautan kasa wato NYSC ta musanta labaran a ke yaduwa akan cewa hukumar ta zabi sabuwar ranan daukan sabbin yan bautan kasa a ranan 16 ga watan Junaru zuwa 4 ga watan Febrairu 2017.
3. Dalibin jami’ar Babcock ya halaka kansa
![Takaitaccen labaran abubuwan da suka faru jiya Alhamis Takaitaccen labaran abubuwan da suka faru jiya Alhamis](https://cdn.legit.ng/images/1120/vllkyt1bqsfud0467g.jpeg?v=1)
Mijin Foluke Daramola, Olukayode Salako, wanda yake da makaranta inda yaron ya karasa karatun sakandarensa, ya daura wannan labari a shafin Facebook din sa . Yace:
4. An cafke mata mai sayar da jarirai a Borno
![Takaitaccen labaran abubuwan da suka faru jiya Alhamis Takaitaccen labaran abubuwan da suka faru jiya Alhamis](https://cdn.legit.ng/images/1120/vllkyt3tj8cl8mettg.jpeg?v=1)
Yayinda rundunar sojin kasa na fafutukan caccakan yan Boko Haram bayan an kwace dajin Sambisa, ashe akwai wani wuta a bagare guda na gidajen sayar da jarirai.
5. Gobara: Kamfanin hada kwalaben Najeriya NBC ta ci bal-bal
![Takaitaccen labaran abubuwan da suka faru jiya Alhamis Takaitaccen labaran abubuwan da suka faru jiya Alhamis](https://cdn.legit.ng/images/1120/vllkyt99i5k5cd162.jpeg?v=1)
Wutan gobara ta tashi a kamfanin hada kwalaben Najeriya NBC da ke Abak ,Uyo jiar Akwa Ibom Game da cewar News Agency of Nigeria,idanuwan shaida sun ce anyi asaran dukiyan miliyoyi a wannan annoba.
6. An damke Sojan bogi da satan babura a Legas
![Takaitaccen labaran abubuwan da suka faru jiya Alhamis Takaitaccen labaran abubuwan da suka faru jiya Alhamis](https://cdn.legit.ng/images/1120/vllkyt4m5ia80dqnf.jpeg?v=1)
Jami’an yan sandan Special Anti-Robbery Squad (SARS) damke wani Wani Sojan bogi wanda ya kasance yana satan baburan mutane a jihar Legas.
7. Wutan lantarkin Najeriya ta haura 4,009MW
![Takaitaccen labaran abubuwan da suka faru jiya Alhamis Takaitaccen labaran abubuwan da suka faru jiya Alhamis](https://cdn.legit.ng/images/1120/vllkyt7b5kai4v336.jpeg?v=1)
Jaridar Vanguard ta bada rahoton cewa kamfanin watsa wutan lantarki wato Transmission Company of Nigeria (TCN) ta bayar da 4,009 megawatts na wutan lantarki ga kamfanoni raba wuta 11.
https://www.facebook.com/naijcomhausa
https://www.twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng