An kama mutane 4 saboda 'Fezbuk'
- An kama wasu matasa hudu a jihar Illinois ta Amurka bayan saka wani video a shafin internit da ke nuna wani farar fata daure ana azabtar da shi
- 'Yansandan Amurkar sun ce suna bincike kan lamarin wanda ya faru a Chicago - abin da ya sa aka kama matasan maza biyu da mata biyu - bisa zargin nuna kiyayya ga wani jinsi
A cikinsa an ga wani saurayi dan shekaru 18 yana neman ceto a kusurwar wani daki an rufe masa baki, an daure masa hannuwa da kafafu, ga kuma alamun yankan wuka a kansa.
A gefe guda kuma aka ga wadannan matasa bakar fata tsaye suna dariya, suna zukar sigari kuma suna yin wasu kalaman batanci ga fararen fata musamman shugaban kasar mai jiran gado Donald Trump.
Bullar wasu karin faya-fayai
Wasu fayafayan bidiyon da aka saka a shafukan internet daga bisani sun nuna yadda aka lakada wa matashin duka, aka sa yasa ruwa daga kasko bawali, kuma aka tilasta masa ya ce ''ina kaunar bakaken fata.
Masu bincike sun ce wanda aka ci wa zarafin abokin daya daga cikin wadan da suka yi masa wannan aikin ne kuma ga alamu sun tsare shi a wurin har tsawo kwana biyu.
Bincikensu ya soma ne bayan an gane shi yana tambele a kan titunan birnin Chicago cikin wani hali na matukar bukatar agaji.
-Ku biyo mu a tuwita: https://www.twitter.com/naijcomhausa
-Ku biyo a shafin fezbuk: https://www.facebook.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng