Abun takaici: Mijin ta ya guje ta saboda wannan dalilin

Abun takaici: Mijin ta ya guje ta saboda wannan dalilin

- Mata masu dauke da cutar yoyon fitsari sun koka da yadda mazajensu su ka guje su saboda cutar da suke dauke da ita

- Majiyar mu ta yi hira da wadansu mata da suke dauke da cutar a wata asibitin warkar wa da kula da masu lalurar yoyon fitsarin 'Evangel Specialist Hospital' da ke jihar Filato

Abun takaici: Mijin ta ya guje ta saboda wannan dalilin
Abun takaici: Mijin ta ya guje ta saboda wannan dalilin

'Cutar yoyon fitsari ya na kama macen da gabobinta bai yi kwari bane sannan kuma ta dauki ciki.

'Idan har hakan ya faru toh ya na iya zama illa ga wannan mata musamman wajen haihuwa.

'Mafitsarinta yakan sami matsalar da ba zai iya rike fitsari ba.

Rakiya Yakubu 'yar shekara 43 kuma mazauniyar jihar Adamawa ta ce ta dade tana fama da lalurar yoyon fitsari.

Tace matsalar yoyon fitsarin ya kamata ne tun mijinta na da rai wanda yanzu Allah yayi masa rasuwa. Tace tayi fama da cutar saboda rashin kudin da zata je asibiti domin neman magani.

Ita kuma Fatima Adamu wanda 'yar shekara 20 ne kuma mazauniyar jihar Bauchi, ta ce a dalilin samun cutar yoyon fitsarin wanda ta samu lokacin haihuwarta na farko, mijinta ya yi watsi da ita inda hakan yasa dolenta ta koma gidan iyayenta domin samun magani da kula.

Bitasi Aliyu ‘yar shekara 21 daga jihar Kano ta ce shekaranta daya a asibitin kuma har yanzu ba ta sami sauki ba. A halin da take tattaunawa da mu ta ce bata san inda mijinta yake ba, sannan ‘yan uwanta sun nuna halin ko inkula akanta.

Hauwa Ibrahim kuwa ‘yar shekara 20 ta ce mijinta da iyayenta suka hada hanu suke biyan kudin asibitinta.

Bayan haka matar gwamnar jihar Fulato Ragina Lalong wanda kwamishanan alamuran mata da kuma cigabansu Rufina Grumyem ta wakilce ta ta zo asibitin domin ta taimaka wa matan da kuma jirajirai da tallafin kayan abinci da na magani sannan kuma uwargidan gwamnan ta yi lale marhaban da jaririya na farko da aka haifa a wannan shekara ta 2017 sannan ta nada mata sunan ta.

Daga karshe uwargidan gwamnan ta ce za ta cigaba da kai wannan tallafi ga yara a asibitocin dake kananan hukumomin jihar.

Ku biyo mu a tuwita: @naijcomhausa

Ku biyo a shafin fezbuk: Legit.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng