Labaran da suka girgiza Najeriya a jiya Litinin
Kamar yau da kullum, Jaridar Legit.ng bata gushe tana tattaro muku muhimman labaran da suka faru a jiya ba ranan Litinin 2 ga watan Junairu 2017
1. Kalli sabon gada mafi tsawo a duniya da kasar Sin ta kaddamar
Kwanan nan, ta kaddamar da sabon gada mai suna gadar Beipanjiang a kudancin kasar bayan an kwashe shekaru 3 ana gina gadan.
2. Wasu yan bindiga sun kashe mutane 4,garkuwa da mutane 30,da kuma sace awakai 250
Wasu yan bindiga kimanin 60 a karshen makon da ya gabata sun kai hari karmar hukumar Rafi a jihar Neja inda suka kashe mutane 4 ,sukayi garkuwa da mutane 30 kuma suka kora awakai 250 daga kauyukan.
3. Ku shirya ma zaben raba gardama - IPOB ta fadawa mambobinta
Kungiyar IPOB tayi kira ga mambobinta a gida Najreiya da kasar waje da su shirya ma zaben raba gardama.
4. Boko Haram: Gwamnatin jihar Borno ta musanta damke shugaban karamar hukuma da aka kama dan Boko Haram a gidansa
Gwamnatin gwamna Shettima tace maganar soji na cewa sun damke shugaba karamar hukumar Mafa ba gaskiya bane.
5. Sabuwar jam’iyya ba zata ba APC tsoro ba - Lasun
Mataimakin kakakin majalisar wakilai Lasun Yusuf ya aika wata sako ga jigogin jam’iyyar APC masu shirin barin jam’iyyar domin kafa sabuwar jam’iyyar.
6. Rikicin Kudancin Kaduna: Za a bude cibiyar MOPOL
Hukumar ‘yan Sandan Najeriya za ta bude cibiyar MOPOL a Garin Kafanchan da ke Kudancin Jihar Kaduna. Wannan yana cikin kokarin Gwamnati na kawo karshen rikicin da ake ta yi tsakanin Fulani Makiyaya da kuma Mazauna Gari.
7. Abunda yasa muka ki sako Zakzaky - Shugaba Buhari
Mai taimaka wa shugaban Najeriya na musamman kan harkar yada labarai, Malam Garba Shehu, ya ce, bai kamata 'yan Shi'a su zargi Buhari ba kan kin sakin shugabansu, Sheikh El-Zakzaky ba.
Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa https://www.twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng