Matan ku rabu da dandalin sada zumunta na intanet ko ku yi hasasar mazajenku

Matan ku rabu da dandalin sada zumunta na intanet ko ku yi hasasar mazajenku

Wani shahararre kuma masani kan amfani da Dandalin sada zumunta da muhawara na internet, ya shawarci matan aure da su rabu da dandalin domin hadarin da ke ka iya jefa aurensu. A cikin wani dogon rubutu da yayi, Mista Dokun Olumofin, ya yi da cewa:

Matan ku rabu da dandalin sada zumunta na intanet ko ku yi hasasar mazajenku
Matan ku rabu da dandalin sada zumunta na intanet ko ku yi hasasar mazajenku

A matsayin mai yawan amfani da Dandalin sada zumunta da muhawara na lura cewa, wasu mata na wuce gona da iri wajen amfani da dandalin, musamman dandalin Instagram da Snapchat da sauransu

Toh, don menene za ki dinga kokarin kara janyo wata matsala ta hanyar barin ‘yan dandalin Facebook da sauransu kutse cikin rayuwar aurenki?

Ga wasu shawarwari uku a matsayin kukan kurciya:

1. Barazanar Tsaro: Duk lokacin da ki ka sa bayani akan makarantar da yaranki suke zuwa, wani taro da ki ka ko za ki halarta, ko aikin mijinki, ko kyautar da yayi miki, da kuma hotonsa yana rike da wani sashi na jikinki, abin da ke saurin jan hankalinsa, misali,

"mijina yana son baka, ko farar mace" ko "mijina na son na yi masa kaza ko kaza" toh, ki sani kamar kin bude kofar yadda mata za su kwace miki shi a waje ne, ko kuma masu satar mutane su sami saukin sace miki yara da sauran su.

2. Kokarin gasa da "yan mata: Ba dai-dai ba ne. Matan aure su dinga gasa da "yan mata wajen kokarin jan hankalin maza a kafafen sada zumunta. Mun san yadda kafafen sada zumunta ke kunshe da kwadayayyun ko shaidanun mazaje, da mata masu rufar kura da fatar akuya.

Mun san kuma yanda wasu mutanen kirki ke kokarin samun mataye na gari a dandalin sada zunmunta na intanet. Mun sha jin labarai kan yadda wasu mutane ke haduwa da abokan zaman su ta kafafen sada zumunta.

Shin ko menene hikimar matar aure ta dinga gasa da yara mata wajen kokarin jan hankalin mazaje yayin da ya kamata ace kokarin jan hakalin mijinta ta ke yi?

Ba laifi cikin shiga mai kyau da mutunci, amma wadannan "yan duniyar suna shigar da idan dai kai ba wani wali ba ne, ko wani Shimfideden Shehi, toh sai sun ja hankalinka na ka tura musu da sakon kai tsaye ko kayi tsokaci ta hanyar da bata dace ba akan abin da suka lika a dandalin.

Wadannan mata na dauke hankalin samari daga samun mata da suka dace. Idan saurayi ya ga hotonki da irin abin da ya ke nema a wajen mace, toh zai yi duk mai yuwuwa wajen ya ga ya ja hankalinki don cimma burinsa.

3. Bude kofar matsalolin aure: Wannan shine ba bban lamarin da na yi imanin yana janyo matsalar sakin aure barkatai. Kasancewar matan aure a dandalin sada zumunta. Sakon kai tsaye zuwa mijinki daga wata mace da taga kyautar da ya baki, kan iya zama hadari.

Wata wacce take takwararki, ko mai kama da ke wacce ta san mijinki, na son mace irinta, (kamar yanda kika nuna), za ta iya kokarin ganin ta ga ta ja hankalinsa, a karshe kuma ta kwace miki shi.

A karshe ina kira gareku matan aure da ku rabu da Dandalin sada zumunta da muhawara na intanet dan kiyaye rayuwar auren ku tare da ganin haske a gidajen ku.

Ina kuma kira ga mazaje da ku hana matan ku shiga dandalin sada zumunta ko kuma wani namiji a waje ya sace hankalin matayen ku a karshe ku ga abin da ba shikenan ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng