Wasu yan bindiga sun kashe mutane 4,garkuwa da mutane 30,da kuma sace awakai 250
- Maianguwan Kusherki Garba Tanko, yace an sace masa akalla shanaye 200
- Sunyi amfani da miyagun makamai wanda ya kunshi bindiga AK47
Wasu yan bindiga kimanin 60 a karshen makon da ya gabata sun kai hari karmar hukumar Rafi a jihar Neja inda suka kashe mutane 4 ,sukayi garkuwa da mutane 30 kuma suka kora awakai 250 daga kauyukan.
Yan barandan wadanda ake zargin yan Boko Haram ne masu guduwa daga dajin Sambisa a jihar Borno sunyi amfani da miyagun makamai wanda ya kunshi bindiga AK47, addunan da sauran su.
Game da cewar jaridan Daily Sun, yan bindigan sun bukaci fana na miliyan2 zuwa miliyan 3 domin sakin kowani mutum daya da akayi garkuwa da shi.
KU KARANTA: Gwamnoni sun shiga taitayinsu
Mallam Ummah Abubakar,daya daga cikin wadanda akayi garkuwa da su yace ya samu arcewa ne da kyar lokacin wadanda akasa suyi gadinsu suka gyangyade saboda gajiya.
Yace bai san inda matanshi biyu Aisha da Maryamu da yaranshi 10 suke ba saboda gaba dayanssu aka dauke.
Wani Maianguwan Kusherki Garba Tanko,yace an sace masa akalla shanaye 200 kuma ya bayyana yadda akaci mutuncin iyalinsu.
Yayinda ba’a samu kakakin hukuma yan sanda domin tofa albarkacin bakinsa ba shugaban karamar hukumar Rafi, Alhaji Gambo Tanko Kagara,wanda ya tabbatar da faruwa yace ya fada shugabanninsa abinda ya faru.
Kana yace za’a dau mataki akan irin wannan kase-kashe da hare-hare kan kauyuka wanda akayi rashin rayuka akai.
Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa https://www.twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng