Janye tallafi da karyar da Naira ba shawara ta bace -Buhari

Janye tallafi da karyar da Naira ba shawara ta bace -Buhari

Shugaba Muhammad Buhari ya kara jaddada kin amincewa da karya darajar Naira da kuma kara farashin kudin man fetur yana mai cewa a kan irin wannan matsayi ne aka hambarar da shi a kan mulkin shekarar 1985.

Janye tallafi da karyar da Naira ba shawara ta bace -Buhari
Janye tallafi da karyar da Naira ba shawara ta bace -Buhari

Shugaban ya kara da cewa a lokacin yana Shugaban mulkin soja kungiyar Bada lamuni ta IMF ta nemi ya karya darajar Naira amma ya ki amincewa da shawarar kungiyar wanda a kan haka ne aka kifar da gwamnati na tare da Garkame ne har na tsawon sama da shekaru uku. yana mai cewa a matsayinsa na Shugaban farar hula, ba zai amince da daukar wannan mataki ba ko da kuwa zai kai ga hambarar da shi daga mulki.

KU KARANTA KUMA: An maka Gwamnatin Najeriya a Kotu

a wani labarin kuma, Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya (NAFDAC) ta ce sakamakon gwajin da aka yiwa shinkafar da jami'an hukumar kwastam na kasar suka kwace ya nuna cewa shinkafar gurbatacciya ce ba ta roba ba.

Wani babban jami'i a hukumar ya ce shinkafar dai na dauke da kwayar cutar bakteriya ne wadda ta wuce adadin da aka amince da ita.

Jami'an hukumar ta kwastam sun hakikance cewa shinkafar da suka kwace a Lagos a makon jiya ta roba ce, lamarin da ya haifar da cece-kuce har ministan lafiya na kasar ya shiga tsakani yana mai cewa ba bu wata shaida da ta tabbatar da hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng