An damke Tsohon sakataren din-din-din na ma’aikatar wutan lantarki akan N1.5bn
- An bayyana Godknows Igali a matsayin ma’aikacin da ya sace motoci SUV 40
- EFCC tace Godknows Igali yayi amfani da wata kamfanin inshore wajen sayen motocin ga kamfen zaben Jonathan
An bayyana Godknows Igali a matsayin ma’aikacin gwamnatin da yayi sama-sama da motoci SUV 40. Hukumar hana almundahan da yima tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta soki Godknows Igali wanda yake tsohon sakataran ma’aikatar wutan lantarki da almundahanan kudin gwamnati.
Jaridar Punch ta bada rahoton cewa EFCC ta gano Godknows Igali ta kudi N1.5bn da ya sayi motoci da su wajen kamfen Goodluck Jonathan.
KU KARANTA: NAFDAC tayi gargadi akan shinkafan roba
Wata majiyar EFCC tace Igali ne wanda akace yana rike manyan motoci SUV a cikin gidansa.
Majiyar tace: “ Igali ya ajiye motoci 47 a wani gida a Abuja amma asirinshi ya tonu lokacin da wani mai gyara ya zo gyara a gidan ya fadawa hukumar EFCC.
“Da wuri hukumar ta fara gudanar da binciken boye. A garin yin bincike ne ta gano cewa kamfamim Dilly Motors ta sayar masa da motocin.
“A wata tura kudi, an biya kamfanin motan N300m daga asusun kamfanin Inshoran Baseworht Insurance. Ma’aikatan hukumar tayi mamakin ta wani dalili zasu yarda kamfanin inshore tayi biyan kudi. Kamfanin Dilly Motors daga baya ta tona cewa N300m din na cikin kudi N1.5bn da aka baiwa Igali ya sayi motoci domin kamfen Goodluck Jonathan.”
Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa https://www.twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng