Dan fafutuka yayi barazanar kai Fayose kotu akan Buratai

Dan fafutuka yayi barazanar kai Fayose kotu akan Buratai

- An umurci Fayose ya kawo hujja akan zargin da yakewa Tukur Buratai na kadara a Dubai

- Dan fafutuka kuma lauya Osuagwu Ugochukwu Esq yace ya baiwa Fayose wa’adin kwanaki bakwai ko a kai shi kotu

Dan fafutuka yayi barazanar kai Fayose kotu akan Buratai
Dan fafutuka yayi barazanar kai Fayose kotu akan Buratai

Dan fafutukan hakkin dan Adam Osuagwu Ugochukwu yace zai kai Fayose kotu akan zargin da yakewa Buratai.

An fada wa gwamnan jihar Ekiti Fayose ya janye maganar sa akan shugaba rundunar sojin kasa, Laftanan Janar Tukur Buratai ko ya gurfana a kotu.

Jaridar Vanguard ta bada rahoton cewa Osuagwu Ugochukwu yayi wannan barazana be a ranan juma’a, 30 ga watan Disamba.

KU KARANTA: Yan sanda masu amsan cin hanci

Yace a wata jawabi da ya baiwa yan jarida a jihar Imo cea Fayose kawai yayi sharri ne akan Buratai cewa yanada dukiyoyi a kasar Dubai ba tare kawo hujja ba.

Saboda haka, Fayose na da daman kwanaki 7 kacal ya janye maganar sa ko kuma ya kawo hujja, in ba haka ba ya fuskanci kiran kotu.

Yace: “Na kalli wannan abin kunyan a tashan AIT yau yadda gwamna Fayode, ba tare da girma ba, yake sukan Janar Buratai da rashawa. Fayose kawai yana Magana akan wasu dukiyoyin Buratai da ke kasar Dubai ba tare da kawo hujjoji akan yadda ya zama mai rashawa.

“Har yanzu ban ga hujjan da Fayose ya kawo ba akan kiran Buratai mai rashawa ba, shin Fayose na tunanin kawai zai soki mutuncin Janar Buratai kuma ya tsira haka kawai?"

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa https://www.twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel