Kungiyar Amnesty International tayi ca akan jihar Edo

Kungiyar Amnesty International tayi ca akan jihar Edo

- Kungiyar Amnesty International tace tayi takaicin abinda gwamnatin jihar Edo keyi na kashe fursunonin a ranan 2 ga watan Disamba

- Kungiyar tayi kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatocin jiha akan daina kashe mutane

Kungiyar Amnesty International tayi ca akan jihar Edo
Kungiyar Amnesty International tayi ca akan jihar Edo

Kungiyar yakin neman yancin dan Adam din, Amnesty International tayi ca akan gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki akan kisan fursunoni.

Kungiyar yakin neman yancin dan Adam din ta soke shi ne akan kisan fursunoni guda 3 a ranan juma’ a 23 ga watan Disamba.

Jaridar Punch ta bada rahoton cewa kungiyar tayi kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatocin jiha su kawo karshen wannan kashe-kashe domin sa ran daina tsattsauran ukuba.

KU KARANTA: Boko Haram ta kai hari mamaya

A wata jawabi ranan Alhamsi, 29 ga watan Disamna, Diraktan kugiyar Makmid Kamara yace aikin jihar Edo ci baya ne akan abinda duniya keyi na haramta ukuba mai tsauri.

Tace: “ Kungiyar Amnesty International tayi ca akan kisan fursunonin gidan yarin Benin City da gwamnatin jihar Edo tayi a ranan 23 ga watan Disamba kuma tana kira ga shugabancin Najeriya da ta dainan kashe fursunoni.

“Muna kira ga gwamnatin Najeriya ,harda jihohin kaar, su daina hukuncin kisa .”

“Kisan da akayi a jihar Edo cibaya akan kokarin da duniya key i na haramta kisa domin kare hakkin dan Adam."

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa https://www.twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng