Muhimman batutuwan da mutan Najeriya suka tattauna akai ranan Juma’ a
Kamar yau da kullum, jaridar Legit.ng ta tattaro muku mu Muhimman batutuwan da mutan Najeriya suka tattauna akai ranan Juma’ a 30 ga watan Disamba, 2016.
1. Fargaba a kwalejin ilimin jihar Adamawa
News Agency of Nigeria ta bada rahoton cewa zuwa awa 1, wannan faruwa ya sabbaba cinkoson motoci a hanyar Jimeta zuwa Yola.
2. Da yiwuwan ‘yan Najeriya mazauna kasar waje zasu fara kada kuri’arsu daga 2019
Shugaban kwamitin majalisar dattawa akan harkokin wajen Najeriya,Sanata Monsurat Sunmonu ta ce zasuyi kokarin yan Najeriya mazauna kasar waje daga 2019
3. Faransa ta sha alwashin cigaba da taimakawa yaki da ta’addanci a Afrika
Gwamnatin kasar Faransa ta aika wata sako ga mayakanta da ke nahiyar Afrika su shirya wa yaki da ta’addanci a yankin
4. Yara 4 da malamar makaranta sun hallaka a jihar Ebonyi
Mutanen Ozizza a Afikpo na jihar Ebonyi sun shiga cikin takaici yayinda wata malamar makaranta da kananan yara 4 suka rasa rayukansu.
5. Ku tafi inda aka tura ku ko ku fuskanci ukuba – Sifeto Janar ga yan sanda
Shugabancin hukumar yan sanda ya gargadi hafsoshi masu kukunai akan turasu aiki da akayi. Shugabancin ta nuna bacin ranta akan rahoton cewa yan sanda 1260 daga yankin kudu maso yamma sunyi zanga-zanga domin an turasu arewacin Najeriya.
6. Bata kare ba: Boko Haram ta kaiwa Soji harin mamaya
Anyi wata batakashi tsakanin rundunar Operationlafiya dole da mayakan Boko Haram da safen nan inda yan Boko Haram 15 suka hallaka.
Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa https://www.twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng