Yadda muke satan kudin mutane kowani lokacin kirismeti - ‘Yan fashi

Yadda muke satan kudin mutane kowani lokacin kirismeti - ‘Yan fashi

- Wasu barayi biyu da aka cafke sun bayyana yadda suke samun issasun kudi domin cin bikin kirismeti

- Barayin sun bayyana yadda suke sane kwastamomin banki

- An cafke su ne yayinda suke je fashi bankin New generation bank kuma suka saci makudan kudi

Yadda muke satan kudin mutane kowani lokacin kirismeti- ‘Yan fashi
Yadda muke satan kudin mutane kowani lokacin kirismeti- ‘Yan fashi

Wani barawo Ugochukwu Nnaji, ya bayyana yadda suke sata kudin banki kowani lokacin kirismeti da sabon shekarar.

Ugochukwu Nnaji na daga cikin wadanda jami’an yan sanda jihar Imo suka kama. Sun kware wajen kwace kudin kwastamomin banki.

Game da cewar Southern City News wadanda suka bayar da rahoton, sun bayyana cewa lokacin Kirismeti da sabon shekara dama lokaci ne na samun kudin Kaman masu kudi.

KU KARANTA: Babbar mota ta murkushe tsohon Sanata

Nnaji yace kudin da suke samu wajen kananan sana’ao’in da suke yi ba zai iashe su wajen sakata da wahalawa ba Kaman masu kudi,saboda haka suka kasance suna fashi.

Nnaji wanda aka cafke tare da abokin aikinsa Chibueze Mgboji a ranan Juma’a 24 ga watan Disamba yace:

“Kowani lokacin biki muke yi,musamman kirismeti da sabon shekara saboda mu sakata mu wahala kamar sauran mutane. Kananan sana’oín da muke yi ba zai sa muji dadi Kaman sauran mutane ba.”

Kwamishanan yan sandan jihar, Mr. Taiwo Lakanu, yayinda yake Magana da manema labarai a hedkwatan su ya tabbatar da cewa an damke barayin yayinda suke kokarin guduwa da kudi.

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa https://www.twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng