Dan kasan faransan da aka kama a dajin Sambisa bakaniken motan yaki ne
- Daga cikin wadanda rundunar Soji suka kama lokacin farmakin Sambisa akwai farin fata
- Bayanan da ake samu yanzu shine farin fatan dan kasan faransa ne kuma kwararre ne
Bayan kasancewansa dan kasan Faransa, farin fatan da aka kama a dajin Sambisa a jihar barno kwararren masanin gyaran motocin yaki ne.
Jaridar Daily Trust game da rahoton ta tace majiyar yan sanda sun bayyana hakan.
Har yanzu dai hukuma hukumar soji bata bayyana hoton baturen da aka kama ba saboda dalilan diflomasiyya,amma rahoton da ake samu daga dan kasan Faransan yana taimakawa na labarai.
KU KARANTA: Tsakanin EFCC da Danjuma Goje
Rahoton tace: “An damke shi a hanyan Bama na dajin Sambisa kuma ya yarda zai bayar da hadin kai idan za’a daga masa kafa.
“Na samu labarin cewa dan kasa Faransa ne amma hukuma bata son bayyana sa saboda dalilai da suka shafi diflomasiyya ……. "
Har yanzu ba’a son yadda ya samu kansa cikin daji ba,amma Kamaru, Nigaer,da Chadi wadanda ke makwabtaka da Najeriya duk masu harshen Faransa ne.
Rahoton tace kasar Faransa bata bayar da amsa akan sakon da aka tura mata ba akan al’amarin
Shugaba Muhammadu Buhari da Soji har yanzu basu daina amsa yabo bat un lokacin da aka samu wannan nasara.
Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa https://www.twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng