PDP ta jinjinawa Buhari kan nasarar kwato dajin Sambisa

PDP ta jinjinawa Buhari kan nasarar kwato dajin Sambisa

- Babbar jam'iyar hamayya ta PDP ta yabawa Shugaban kasa Buhari biyo bayan nasarar da sojin Najeriya suka samu ta fatattakar Boko Haram tare da sake kwato dajin Sambisa

- PDP a ranar 24 ga watan Disamba, ta aika da sakon taya murna ga sojojin Najeriya a kan nasarar da suka samu a kan masu ta da kayar baya wanda ya kai ga kwato sansanin da sojin suka yiwa lakabi da "Camp Zero" da ‘yan ta'addan suka dinga amfani da shi

PDP ta Jinjinawa Buhari kan nasarar Kwato dajin Sambisa
PDP ta Jinjinawa Buhari kan nasarar Kwato dajin Sambisa

Babbar jam'iyar hamayya ta PDP ta yabawa Shugaban kasa Buhari dangane da asarar da rundunar sojin Najeriya ta samu na fatattakar Boko Haram tare da sake kwato dajin Sambisa.

A wata sanarawa da Sakatarenta na yada labarai na kasa, Prince Dayo Adeyeye yayi, PDP ta taya sojojin Najeriya murna.

Sanarwar ta kuma ce, nasarar da aka samu sakamako ne na kokarin tsohon Shugaban kasa, Good luck Jonathan, wanda yayi duk mai yiyuwa dan tabbatar da cewa zabe ya gudana a yankin a shekarar 2015.

Karanta jawabin dake kasa:

1- Kwanaki kadan da suka gabata, sojojin Najeriya sun bayyana nasarar kwato dajin Sambisa wanda ke zama babbar maboya ta karshe ga ‘yan Boko Haram. Wannan babban ci gaba ne a yakin da ake da fama da ta'addanci.

2- Muna taya "yan Najeriya murna akan wannan babbar nasara mai muhimmanci a wannan yaki mai tsawo da akeyi da wadannan mugayen mutane da suka jawo damuwa da wahalhalu masu tarin yawa ga al-umar mu a shekarun da suka gabata.

3- Muna taya Shugaban Kasa murna kan jajircewar da yayi tare da ci gaba da yakar masu tada kayar baya. Munyi farin cikin dorawar da yayi akan kokarin da magabatan sa suka fara. Duk nasarar da muke gani a yau sakamako ne yunkuri da sadaukarwa da tsohon Shugaban Kasa yayi.

Mutanen Najeriya dama na kasashen waje ba za su manta da kokari tare da nasarar da aka samu ba, makwanni kadan kafin zaben shekarar 2015.

An samu babbar nasara akan Boko Haram, nasarar da ta bada damar gudanar da zaben 2015 a kusan daukacin kananan hukumomin da ke jahohin Arewa maso gabas. Muna matukar farin cikin dorawa da Shugaban Kasa yayi akan wannan kokari.

4- Muna jinjinawa sojojin mu maza da mata. Jarumta, niyya tare da sadaukarwar su ita ce ta kawo ga wannan nasara. Sojin Najeriya sanannu ne a duk fadin duniya a ayyukan samar da zaman lafiya. Muna jinjina musu sabo da tsayawar da suka yi dan tabbatar da zaman lafiyar kasar su.

5- Muna kuma godewa kasashen waje sabo da taimakawar su da karfafa gwiwa musamman ma wanda suka taimaka da makamai ga sojojin mu.

6- Kwato Dajin Sambisa babbar nasara ce amma fa ba shine karshen tada kayar baya ba. Gwamnati da sojoji dole ne suci gaba da wannan fafutuka babu kakkautawa har sai baki daya an kakkabe "yan ta'adda daga yankin Arewa-maso-gabas.

7- Bayan Sambisa, duk sauran gurare da "yan ta'adda ke amfani dashi a matsayin mafaka da sansanoni dole a kwato su. Gurare irin su Birnin Gwari, Zamfara, kudancin Kaduna, Enugu da Benue sun zama filin kisa. Dole ne a kakkabe duk wani burbushin aikin laifi a cikin su.

8- A wannan lokaci na bikin Kirsimeti, muna kira ga duk "yan Najeriya da su yi fatan alkhairi ga juna. Fiye da kowanne lokaci a baya, dole ne mu hada kai da tabbatar da zaman lafiya da hadin kan kasar mu wacce bamu da wata kamarta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng