Dokar daidaita rabon gado tsakanin maza da mata ba zai yiwu ba – Sultan Sa’ad Abubakar lll

Dokar daidaita rabon gado tsakanin maza da mata ba zai yiwu ba – Sultan Sa’ad Abubakar lll

- Sarkin musulmi Sa’ad Abubakar lll ya tofa albarkacin bakinsa akan sabuwar dokar ake yunkurin kawowa

- Dokar ta bukacu a daidaita rabon gado tsakanin maza da mata

- Yayi kira ga majalisar dattawa suyi watsi da wannan doka saboda matsalolin addini

Dokar daidaita rabon gado tsakanin maza da mata ba zai yiwu ba – Sultan Sa’ad Abubakar lll
Dokar daidaita rabon gado tsakanin maza da mata ba zai yiwu ba – Sultan Sa’ad Abubakar lll

A ranan Talata, 27 ga watan Disamba, Sultan na Sokoto Alhaji Sa’ad Abubakar lll,ya tofa albarkacin bakinsa akan yunkuri daidaita rabon gado tsakanin maza da mata.

News Agency of Nigeria ta bada rahoton cewa Sultan ya bayyana hakan ne a Gusau wajen taron kulle gasar karatun Al-Quráni karo na 20 inda yace wannan doka ta sabawa karantarwan addinin musulunci, saboda haka, musulmai ba zasu yarda da shi ba.

KU KARANTA: Matasa sun jinjinawa Buratai

Dokar tana bukatann ayi daidai wa daida tsakanin maza da mata a waje rabon gado , kana kuma mace ta samu hurumin tafiya da yaranta idan sun rabu da mijin sai dai idan yaran ne basu so.

Kana dokar na bukatan matar da ta rasa mijinta ta sake auren namijin zabinta kuma tanada hurumin raba gadon mijin biyu kuma tanada hurumin zama a gidan mijin.

Abubakar yace: “Addinin mu rayuwa ce gaba daya; saboda haka, ba zamu yarda da canza abinda Allah ya halalta mana yi ba.

“Addinin Islama addinin zaman lafiya ne; mun kasance cikin zaman lafiya da kiristoci da kuma mabiya wasu addinani. Saboda haka, a rabu da mu domin aiwatar da addinin mu sosai.”

Saboda haka yayi kira ga majalisar dattawa tayi watsi da wannan doka saboda addini.

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa https://www.twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel