Gimbiya Siddika ta shiga gidan Miji a Katsina (Hotuna)
Gimbiya Siddika ‘yar Mai martaba Sarkin Kano ta tafi gidan miji a Katsina a wani kasitaccen biki da aka yin a kai amarya da aka yi a ranar Litinin25 ga watan Disamba 2016.
A ranar Lahadi, 25 ga watan Disamba ne aka kai ‘yar Mai martaba da Sarkin Kano Muhammadu Sunusi Gimbiya Siddika dakin miji bayan shafe mako guda da aka yi ana bikinta a Kanon Dabo.
Wani ma’abocin dandalin sada zumanta da muhawara na Facebook Alhaji Bashir, wanda kuma yana daga cikin ‘yan rakiyar amaryar ne ya sa hotunan isar Gimbiyar garin Katsina.
KU KARANTA KUMA: Dan sanda ya kashe wani matashi ana saura kwanaki 5 aurensa
Gimbiyar ta isa Katsina ne a inda aka fara kai ta gidan Sarkin Kano da ke Katsinan a mota, kafin a kai ta gidan miji a kan Doki tare da ‘yan rakiya a bisa al’ada, kamar kuma yadda Bashir ya rawaito.
A wani labarin kuma a yayar Gimbiyar ta haifarwa da Mai martaba Sarkin jika a ranar da aka daura auren Siddikan a Kano.
Ku cigaba da bin mu a shafukan sada zumunta na Tuwita @naijcomhausa
Asali: Legit.ng