Yadda Sojoji suka ci Sambisa da yaki (Hotuna/bidiyo)
An fitar da wani faifan bidiyo dake nuna yadda mayakan rundunar sojan kasa suka ci dajin sambisa da yaki yayin da suka fatattaki mayakan rundunar Boko Haram.
Wata kungiyar jam’iyyar APC reshen kasar Landan ce ta fitar da faifan bidiyon wanda ke nuna irin jarumta, kware da sanin makaman aiki da sojojin Najeriya suka nuna yayin da suka kai samame mai karfi zuwa cikin tsakiyar dajin Sambisa, inda mayakan Boko Haram ke boye.
KU KARANTA: Hukumar Sojin kasa ta fara gina hanya zuwa dajin Sambisa
Wannan harin da sojoji suka kai shine ya kawo karshen tarewar mayakan rundunar Boko Haram a cikin dajin, an kwashe sama da wata daya ana kokarin fatattakar yan Boko Haram din daga dajin, inda rundunar mayakan sojan kasa ta aika da sojoji 4,200 ta hanyoyi da dama, kamar su Ngurosoye, Konduga/Aulari, Bama, Fulka da Damboa.
Ga kadan daga cikin hotunan harin da sojoji suka kai dajin Sambisa:
A wani labarin kuma, hukumar mayakan sojan kasa ta tabbatar da kama wani mutum farar fata a dajin wanda ake tunanin yana taimaka ma kungiyar Boko Haram.
Wani rahoto daga gidan talabijin na kasa wato NTA ya ruwaito wani jami’in soja wanda da shi ne aka kai harin yana cewa sun kama farin fatar ne a ranar Alhamis 22 ga watan Disamba bayan sun ci dajin Sambisa da yaki.
Ga bidiyo a kasa:
Asali: Legit.ng