Tashin hankali : Rundunar Soji sun kama bature a dajin Sambisa

Tashin hankali : Rundunar Soji sun kama bature a dajin Sambisa

- Wani jami’ain soja wanda yayi musharaka cikin kwato dajin Sambisa yace an damke wani bature a mabuyar Boko Haram

- Majiyar tace an kashe mayakan Boko Haram daruruwa kusan wata daya yanzu

- Sojan ya bayyana cewa hukumar soji ta tura dakarun soji 4,200 cikin dajin Sambisa

Tashin hankali : Rundunar Soji sun kama bature a dajin Sambisa
Tashin hankali : Rundunar Soji sun kama bature a dajin Sambisa

Hukumar sojin Najeriya ta damke wani bature a cikin yan Boko Haram din da aka kama a dajin Sambisa.

Wani jami’ain soja wanda yayi musharaka cikin kwato dajin Sambisa yace an damke wani bature a mabuyar Boko Haram.

Game da cewar gidan talabijin NTA, sojan bai bayyana ko dan kasa bane baturen. An damke shine a ranan Alhamis,22 ga watan Disamba.

KU KARANTA: Jirgin saman kasar Rasha tayi hadari

Sojan ya fasa wannan kwai ne a yau lahadi,25 ga watan Disamba, inda yace an hallaka daruruwan yan Boko Haram kimanin wata daya yanzu.

“An hallaka daruruwan yan Boko Haram,maza da mata da yara kuma an ceto su kuma an kaisu inda zasu tsira.

“Abunda zan iya fada muku shine babu wani kwamandan Boko Haram da ke da rai a dajin Sambisa; mun kwace dajin gaba daya.

“Ya dauke mu watanni domin shiryawa wannan farmai, girman daji,yanayi da wasu abubuwa ne suka jinkirtar da mu.”

Ya kara da cewa abinda ya jinkirta kwato dajin shine yan Boko Haram na amfani da kauyawan da ke cikin dajin wajen garkuwa.

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa https://www.twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel