Da kudin Oscar, zamu siyo wadannan yan wasan (Karanta)

Da kudin Oscar, zamu siyo wadannan yan wasan (Karanta)

Wasu rahotanni na nuna cewa kocin Chelsea Antonio Conte zai yi amfani da fan miliyan 60 da suka samu a cinikin sayar da Oscar ga Shanghai domin sayo 'yan wasa biyu daga Monaco.

Kamar yadda rahotannin suka nuna 'yan wasan biyu da Chelsea ke son saye daga kungiyar ta Faransa su ne Tiemoue Bakayoko da Dijibril Sidibe.

Da kudin Oscar, zamu siyo wadannan yan wasan (Karanta)
Da kudin Oscar, zamu siyo wadannan yan wasan (Karanta)

Kocin na Chelsea ya yi tattaki zuwa Faransa tare da darektan kwallon kafa na kungiyar Michael Emenalo domin ganin yadda Bakayoko da Sidibe suke taka leda

Bakayoko dan wasan tsakiya da kuma Sidibe, dan wasan baya sun taka leda a wasan da Tottenham ta yi da Monaco na gasar cin Zakarun Turai, ranar 22 ga watan Nuwamba, na 2016.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Kaduna ta kafa dokar tabaci a wadannan kananan hukumomin

A wani labarin kuma, Kotun daukaka kararrakin wasanni ta duniya ta rage hukuncin hana Real Madrid sayen 'yan wasan tamaula zuwa kakar wasa daya.

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ce ta yankewa Madrid hukuncin hana ta sayo 'yan wasan kwallon kafa zuwa kakar wasanni biyu, bayan da aka same ta da laifin karya ka'ida.

Sai dai kuma hukuncin na nufin Madrid ba za ta sayi 'yan wasa ba a watan Janairun nan a lokacin da za a bude kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo har sai karshen kakar bana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel